Kauna ce sila 31
*KAUNA CE SILA💝*
*written* *by* *:* *khadijah* *Tijjani*
*31*
Daga kallo daya ya fahimci yunwa ke addabarta...kin fara serving punishment naki, ya fad'a yana murmushin mugunta
Bai tausaya mata ba yana ganinta yashe a k'asa ya ciro snacks cake kwaya biyu a side drawer'nshi da ruwa a fridge ya jefo mata yayi abunda zaiyi ya shirya tsab ya fita tare da rufe kofar ta baya kamar yanda yayi jiya
Da kyar ta samu ta mike ta dau snacks din ta fara ci, abu mai dumi da zai warware mata ciki take bukata amma tasan bazata samu ba, wannan ma tasan idan ta bari yunwa illata ta zaiyi ta Sani ba shakka gwara ta lallaba ta rage wa kanta azaba
Kamar wata mayya haka tayi ta cin bushashen cake ta gama ta bi shi da ruwan gora tas ta shanye gora daya
•••••
Shi kuwa yana fita side d'in Mamababba ya wuce
Sallama yayi tare da shigewa parlour'n ta straight dinner ya wuce ganin warmers a jere wajen ko gaisuwar yau bata samu arzikinshi ba
Yana bude flasks din kuwa favorite nashi ya gani aciki, sinasir na miyan kub'ewa...zama yayi ya cika cikinsa tab tukun yayi hamdala ya mik'e tare da isowa inda take
"Matar ya naganki sukuku haka, what's wrong??ya tambaya tare da zama gefenta
" Yau kuma ra'ayin naka bai ce kayi gaisuwa ba kenan, tukunna wa ya baka izinin cin abincina...
"C'mon matar da abincin naki da ke kanki duk ba nawa bane...zaki fara mitar naki ko ki bata min rai yanzunnan kuma ki hadu da fushin mala'iku ba...ya fada tare da kashe mata ido
" Dalla ni bani da lokacin wannan wasan, wallahi duk a kidime nake..yanzu Zaitunah ta kawo min breakfast take fad'a min forhaana kawartan nan yar gidan Antynku Bilkisu ne ta bata ba'a ganta ba, yarinya yar kirki karama da ita wallahi abun tausayi... Ta labarta masa har da d'an matsar kwallanta
"Hoo, hajiya wannan yarinyar kina ji da ita tunda naga yanda kika damu da batun..
Shi duk zatonsa bai zo kan yarinyar da ke garkame dakinsa ba kuma gashi MamaBabba tace yarinya karama shi kuwa yasan yarinyar wajensa babba CE infact shi ya ma manta da wani yarinyar da yake rike da ita
"Babana dole na damu, ba'a fa san halinda yarinyar nan ke ciki ba..
Kwantar da hankalinki matar, InshaAllah za'a same ta..I assure you that" ya fada dan ya lallasheta
" kwana2 ban hadu da Ummi na ba, Bari na je na dubo ta..
" INA fa zaka ganta, mahaifiyarka ai ta je gidansu yarinyar tunda ta ji labari dazu da safe..da ita ake ta cigiyar, tana bala'in son yarinyar ai
"Ummi da son yara yanzu nasan sai tayi ta wahalar da kanta akan batan yarinyar nan duk ta hana kanta sukuni...Allah dai ya bayyanar da ita, ya fada tare da mikewa yayi hanyar fita
" Amin ya rabbi..ta amsa
Yana fita wajen parking lot ya nufa, ya shiga motarsa kirar jeep though Mercedes Benz fara sol ya sha tint zai ja yaga Ameer ma ya shigo gidan kuma ga dukkan alamu shima hankalinsa a tashe yake
Bai zata abunda zai ji shima daga bakinshi ba shiyasa ya tambaya shi, thesame story yayi narrating masa kamar yanda Mamababba ta fada masa
"Wai wacece wannan yarinyar da kowa ya tada hankalinshi akanta...ya tambaya a d'an fusace
Bayani Ameer ya masa, ya so ya gano ta amman rabonshi da ita tun batayi wayo ba lokacin da suka tafi makaranta
" Allah ya sa a sameta, abunda ya dad'a fada kenan
Kamar mai jira kuwa Ameer da sauri ya Amsa da "Amin, alamunshi ya nuna ya ji dadin addu'ar
" come, come here boy! Ko dai ko dai?? Anya ba boyayyen al'amari
Behzad ya tambaya with smily face
Ameer sosa keyarsa yayi tare da yin murmushi yayi shige ciki, shi kuwa behzad tayar da motarsa yayi ya wuce company'nsa already sunyi waya da Habib and Anas akan can zasu hadu yau......
Comments
Post a Comment