Kauna ce sila 33.34.35
[9/27, 9:17 PM] Sis Salmat: *KAUNA CE SILA💝*
*written* *by* *:* *khadijah* *Tijjani*
*34*
•••••
Can gidan su forhaana kuwa anyi cigiyar anyi har sun gaji ba labari sai kawai suka dukufa wajen Malamai akan a taya su da addu'a Allah ya bayyanar da ita kuma duk an basu tabbacin nan ba da jimawa ba zata bayyana..
Zaitunah da Ummin behzad kuwa tun da abun ya faru ba Kansu suna can gidansu forhaana ana ta cigiyar da su haka zasu wuni zagaya gidan abokan arziki da yan'uwa ko za'a sameta da daddare kuwa su kwana addu'a da nafilfila
Amarai kuwa suna can gidajensu ba wanda ya fad'a musu ko ya basu lbrin abunda ya faru dan gudun tashin hankalinsu..
••••
Zaune suke a parlor'n gidan, Ammin, Ummin behzad, Zaitunah, AuntyFatii(matar kawunsu Zaitunah) sai mahaifiyar Zaitunah AuntyZainab duk sunyi jugum kowa da abunda yake ayyanawa cikin ransa
"Assalamu alaykum"... Ta kwala sallama tare da shigowa ciki da d'an gudunta
Gaba daya sun gane muryar ta..har rige rigen fita suke su tabbatar wa idonsu abunda suka ji ai kuwa turus sukayi ganin forhaanan CE kamar yanda suka ji
A guje ta fad'a kan Amminta ta saki kuka, duk sun rikice sai sannu suke mata
Gaba dayansu sai hamdala suke tayi, komawa sukayi suka zauna cikin parlor babu wanda ya tambayeta mai ha faru ganin duk itama kamar ba a nutse take ba...ita kuma da gangan duk ta hargitsa kanta dan su fi yarda da abunda zata fad'a
Bayan ta huta tayi dad'a yin wanka ta sake cin abinci suna zaune a parlor Ammi take tambayarta abunda ya faru ai kuwa ta hau hawaye tana basu labari....
"..... _bayan na samu na gujewa AntyNaana ne na fita bakin layi dan in tare cab da zai kaini gida ganin already mutanen da suka kawo mu sun koma, na fita ban samu ba kusan 1h INA abu daya har na gaji na fara kiran gida a zo a kaini kawai sai wasu maza su hudu a mota suka tsaya wai zasu rage min hanya naki shiga na fara tafiya da k'afa bansan lokacin da dayansu ya fita ya daukeni cidak zai sakani cikin motar ta su ba na fara ihu kawai sai naji ya danna min abu a hanci ban kuma farkawa ba sai a wani gidan da ba zan iya kwatanta shi ba dan ban taba samun fita daga cikin dakinda suka sakani ba..haka na zauna banda ruwa da cake kwaya 2 sai in wuni ba abunda nake samu kuma ban taba ganin wani ya shigo ba sai dai su wurga min su sake rufo kofar haka har yau an waye gari hayaniyarsu ya tayar da ni suna fad'a akan wasu sunce banida amfani wajensu while sauran kuma sunce a bar musu kawai ogan nasu ya yanke hukunci akan su je su wurgar da ni bakin hanya..basu da ta cewa kuwa naga an budo kofar suka daure min fuska da farin kyalle suka sakoni cikin mota muna ta tafiya kusan minti30 kuma suka tsaya suka cironi suka ajiyeni bakin hanya sukayi gaba abunsu_
Duk sunyi shuru suna sauraronta banda ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un babu abunda suke
Ta ci gaba..
_ina samun nutsuwa kuwa na bude idanuna na mike zuwa kan hanya na fara tare motar da zai taimaka ya kawo ni gida kusan 30mins kuwa shuru ban samu ba sai daga baya na samu wani motar ya tsaya taimako na, nayi banza da shi dan gudun fadawa cikin irin abunda na samu na kufud'a ai kuwa ya sauko har zan gudu kuma sai naga Ashe Yah behzad ne..toh shine fa ya taimakeni ya kawo ni gida shima ban fad'a masa abunda nakeyi wajen ba kawai CE masa nayi na tashi daga gidan yar'uwar Abba ne_
ta kareshe basu labarin tana hawaye..irin su dad'a amincewa da batunta
Gaba daya kuma maamakin kanta take yanda ta tsara karya haka, ko dayake ba dan shi tayi ba sai dan Mamababba da Umminsa dan tasan idan har mahaifiyarsa taji abunda yayi ranta ba karamin baci zaiyi ba..
Gaba dayansu sai sakin Alhamdulillah a tare suke jin basu wani illata ta ba Allah ya kareta sai kuma addu'ar Allah ya kare gaba..
Shigowar Abbanta kenan aka labarta masa kamar yanda forhaana ta fad'a musu
Shima Hamdala yayi tare da godiya ga Allah da yasa basu cutar da ita ba dan daga ji ba mutagen Alkhairi bane sai kuma faman saka wa behzad Alkhairi suke..
© *deejatou*
[9/27, 9:17 PM] Sis Salmat: *KAUNA CE SILA💝*
*written* *by* *:* *khadijah* *Tijjani*
*33*
Suna rabuwa straight gida ya wuce, yana shiga falon bangaren kuwa abunda ya gani ne ya sa shi shan jinin jikinsa..MamaBabba ne zaune gefenta forhaana da cup din tea a hannunta tana shaa
Wani wawan kallon da ta watsa masa kuwa sai da ya kusan zaucewa
Ya akayi tasan da mutum cikin dakincan kuma? Yake ta tambayar kansa
"Ai sai ka karso kuma ba..ko haushi kaji baka samu ka cimma burinka ba, ka zo ka sameta da ranta..eyyeh?... Ta hasale tayi maganar
Dak'ewa yayi ya karaso ciki tare da zama kusa da mutuniyar tasa, ya juyo rai bace yana kallon forhaana yace"kee! mai ya ciro da ke daga cikin dakin, so kike inyi doubling miki punishment din naki ko..yana maganar ne amma duk a dak'e yake yi dan yasan sarai mamababba CE ta bude ta dan ta baya ya rufo kofar kuma yasan sarai akwai spare keys wajenta
" in ka kuma bude bakinka wajennan duk gidannan sai sun San abunda ka aikata daga kan Kkadijatu har kawunka gaba daya wallahi
Ai karaf kamar ruwa ya cinye sa yayi shuru forhaana na ganinsu abun har dariya ya so bata kasancewar yanzu tayi wanka ta ci abunci nak babu abunda ke damunta sai son ta tafi gida wajen iyayenta
"Yanzu fisabillah mai baiwar Allahn nan tayi maka ka kama ka kulleta a daka ba ci mai kyau ba sha, gaba daya a dalilin abunda kayi ka sa duk yan'uwanta tashin hankali..yanzu ba dan na jiyo karanta ba INA zan San akwai mutum ciki duk ta galabaita yunwa tana neman mata illa dan shakiyanci kuma kana ji ranan mukayi maganar Batan ta da kai baka ko nuna min alamun kasan inda take ba ma shegen yaro"...mamababba take masa fad'a kamar ta ari baki
Sai yanzu ya fahimci cewa wannan yarinyar ita ce duk gidan suka tayar da hankalinsu akanta har Umminsa
" Yah rabbi..he's already confused
Mai yasa ma ni na dauke ta ne, kai da ma ban taimaketa ba tun fari gashi zata ja min bakin jini cikin yan'uwa na
Hakuri ya bawa Mamababba sannan ya fad'a mata dalilinsa na yin hakan"ai ita ma ya kamata kiyi wa fada ba ni ba in dai bin gaskiya ne...a shagwabe yayi mata magana shima duk dan ya kashe batun
"Gafara dalla, Allah ya sa bulala ta dauka ta dakeka ba mari ba..mamababba ta fad'a duk har yanzu tana fushinta
Forhaana na ganin dramar da suke tayi, ta kula ran mamaBabba ya baci ne yasa ta kwantar mata da hankali akan ita ta ma hakura tun tuni yanzu gda take son zuwa dan tasan duk hankalinsu ba a kwance yake ba
Karaf ya mik'e tsaye yana fadin" saura kuma in kin je gidan naku ki ambaci sunana wallahi sai na shak'e ki kin halaka gaba daya dan ni na sa'an wasanki bane wannan ma tsautsayi ne..
"Yoo in ban ce kai ka saceni ba ni wani uwar karyar zan musu kuma..gaskiyar zancen kenan ka saceni ka kawo ni dakinka ba ci ba sha tsab abunda zan fad'a musu kenan"...a tsiwace ita ma ta tsatse shi, da gangan kuma ta fad'i hakan dan taga ya zaiyi reacting
" yauwa jikalle ta, fad'a musu gaskiyah..in ya so sai shi yaje ya musu bayanin dalilin da yasa ya aikata hakan...Mamababba ma tayi supporting nata
Gaba daya zufa ke karyo masa, shi yanda yake kallon girman Auntybilkisu da mijinta su ma suke mutunta sa kamar wani Babba wannan shegiyar yar tasu zata zubar masa da girma wajensu...shi dai Ego dinsa da pride NASA bazasu barshi ya roketa akan ta rufa masa asiri ba gashi Wannan tsohuwar ma sai faman zugata take ta yi
"Yanzu dai koma menene ki saurareni, kada ki kuskura inji kin saka behzad cikin wannan shirmen naki..ya daure fuska tare da shaida mata
" yau ni dai na ga ikon Allah, toh so kake ta CE wa iyayen NATA ita ta dauke kanta ne ko mai?
"Atoh kaka taya ni tambayarsa...forhaana ta karkada kanta ta fad'a
" ni dai na Riga nayi warning naki...ya wuce dakinsa ba tare da ya sake magana ba
Hakuri MamaBabba ta ta bata akan abunda yayi mata ita kuwa sai hana ta bata hakurin take dan tasan ba a saninsu ya ajiyeta ba d'an tana da tabbacin son da bayin Allahn nan suke nuna musu daga ita har iyayenta..tsab ta shirya akan zata tafi gida dan bata son kowa yasan tana cikin gidan ko mai yasa? Oho mata
Ta fito daga bangaren bayan sunyi sallama da Mamababba ta sulale a hankali ta bar cikin gidan ba tare da kowa ya ganta ba...
© *deejatou*
[9/27, 9:20 PM] Sis Salmat: *KAUNA CE SILA💝*
*written* *by* *:*
*khadijah* *Tijjani*
*35*
Yau kwanan ta uku a gida gaba daya kowa ya koma harkan gabansa tare da addu'ar Allah ya takaitar a kan wannan..
Anas da Habeeb sun zo gidan nasu sun sameta a washe garin zuwanta gida tayi mishi bayanin cewa wayarta ne ya bata shiyasa yaji ta shuru amman ta karba NASA akan zata kira sa bayan yayi yayi da akan zai kawo mata tace A'a baza'a barta a gida ba..
Haka ya hakura ya koma bayan sun taba hira kasancewar yanzu tana yinsa ba laifi, sun wuce akan sai ya ji ta har ya tafi kuwa bai hadu da mahaifinta ba..
Behzad kuwa daurewa kawai yakeyi amma hankalinsa ba a kwance yake ba tunda ta tafi kullum yana jiran yau ne za'a zo neman sa, gobe ne shuru dai har yau tukun yaji kiran mahaifinta daga wajen Ameer da yaje gaishe shi da mishi barkan bayyanar forhaana
Dam! Gabansa ya fad'i, shi gaba daya ya dauka akan abunda yayi wa diyarsa yake nemansa...I'm stupid enough tunda har na dauka bazai dauki mataki akan abunda nayi wa yarsa ba
Da yammacin ranar ya buga motarsa ya tafi gidan da kyar mmya gane hanya kasancewar ya jima rabonsa da gidan..kai tsaye ya shiga da motarsa yayi parkinga sannan ya shigo cikin apartment na farkon da ya fara cin karo da shi kuma yayi sa'a nan ne mahaifinta yake
Sallama yayi yana tsaye kusan minti 5 ba wanda ya amsa masa sai ya wuce straight ya nema wa Kansa masauki cikin jerin kujerun da ke shinfid'e falon
"Ba laifi, tsarin parlorn yayi masa kyau..a ayyana a ransa
Fitowanta kenan itama daga kitchen ta gama had'a abincin daren zata jera kan dinning table dake dayar bangaren falon da aka keb'e ya zama dinning area
Tana sanye cikin apron fari tas kamar ba aiki tayi da shi ba ta fito taana jin wakarta a earpiece dake manne a kunnenta
Karaf ta hango shi yana zaune amma hankalinsa na kan wayarsa...kare masa kallo tayi duk da yana zaune from head to toe, he gt everything amma banda hali...ta fad'a tana murguda baki
Shima karan ajiye Warmers da plates da takeyi ne yasa shi sanin akwai mutum wajen. Yana juyowa kuwa gabansa ya fad'i shikenan yau a gaban wannan yarinyar za'a wanke shi...Allah ya sa dai abun ya zo cikin ruwan sanyii
" Amin..ya amsa wa kansa
Bai kuma ganin ta ba, kuma yaji wurin shuru alamun ta bar wajen..after some minutes mahaifinta ya fito yana ganinsa ya fad'ad'a fara'arsa, gaba daya ya daure ma behzad kai ganin yanda ake ta masa hab'a hab'a cikin gidan har Auntyn tasa
Daga karshe kuma suka masa godiya ga kawo forhaana gida da yayi ana ne ya fahimci duk abunda suke nufi bayan sun bashi labari kamar yanda ta basu
Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke...but why?? Ko dai ta tsorata da ni ne ya sa ta rufa min asiri, eh mana..ai nayi maganinta..sai wani bubbudawa yake a dole shi yayi abun kirki..
Sun d'an taba hira kenan aka kira sallar maghrib suka fita masallaci da mahaifinta suyi sallah ita kuwa daman tun da ta shige daki bata fito ba har tayi sallarta itama lokacin su ma sun idar sun komo gida
Around 7:00pm ya tashi a nufin zai tafi gida amma fir Abban forhaana yace ya bari suyi dinner tukun ya wuce..ba yanda ya iya haka ya yarda
"Bari na kira forhaana mu hadu muyi dukkanmu, inji Ammi tare da wucewa zuwa dakin forhaana ta kirata
" wato shi riba biyu ko, ya samu godiya ga garar abinci..toh ai sai dadin ya masa yawa... "Forhaana ta fad'a a ranta jin harda shi za'a ci abincin da ta sha wahala ta tsara musu ita da iyayenta
" kiyi sauri ki samemu kamun nayi serving nasu..
Koh mai ta tuna kuma tayi saurin katse Ammin
"Muje ma kawai Ammi ai na gama..ta fad'a
Yauwa"
Suka fito a tare already har behzad da Abba na kan table suna jiransu tare da d'an taba hira akan Medico..
Gaishe shi tayi d'an kar su Ammi su fahimce ta
Ya amsa kuwa kamar sunfi kowa shiri nan duniya..ita kuma ta dauko serving spoon ta fara serving nashi fuskarta taf dauke da murmushi
Sai da ta tsoma serving spoon din cikin jaan borkononta mai zafi da take cin abinci da shi dan akwaita da son yaji tukun ta diba mishi ba tare da kowa ya kula da abunda takeyi ba sai faman lafta masa borkono take cikin abinci ta jujjuya tsab kuwa sannan ta diddibawa su Ammi da Abba ta mika wa kowa itama ta saka nata gaba sukayi bismillah a tare suka fara ci....
© *deejatou*
Comments
Post a Comment