Kauna ce sila
[8/19, 6:43 PM] Deejatou: *KAUNA CE SILA💝*
*written* *by* *:* *khadijah* *Tijjani*
*17*
Tsayawa yayi yana kare mata kallo...dubeta dai yarinya ba wata babba ba amma ta iya karfin halin daga masa murya ko tsoro bataji, abun nata yanzu haushi ya fara basa...ya dai kamata ya nuna mata no one mess with _Behzad Marwa_....cikin ransa yake maganan nan
Ganin ya manna mata abun ya dad'a bata haushi..a hatsale ta ce
"Ai kuwa wannan ba rashin iya mota ke damunka ba, rashin sanin mahimmancin dan Adam ne, kai inaga har da ma rashin tarbiya idan ba haka ba ta ya zaka yi wa mutum laifi ka tsaya kana mishi kallon tsiya...
"Whaaaaaat???
"Mai kike fada, how dare you! Kina da hankali kuwa?? Waye sa'anki nan wajen zaki tsaya kina gaya min magana.. Ya fada yana wani zazzaro ido shi a dole ransa ya baci
"An fada maka...rashin tarbi....
Bai bari ta karasa batun nata ba ya wani zabga mata uban marin da sai da wurin gaba daya ya dauka..
Waiiii, ji tayi jijiyoyin jikinta sun damke waje daya, zafin marin yasa taji kanta ma yayi mata nauyi..ta kai minti 2 kanta na k'asa bata dago ba.
Shi kuwa yana tsaye sai faman huci yake, har an haife macen da a duniya zatayi masa irin rashin kunyar nan ya barta ne!....jira yake kawai yaga next action nata dan ya tabbata taji zafin marin
Sai da ta bari ta komo normal tukun ta dago kanta...ba tare da tsoro ba ta dan dago kafarta dan yayi mata tsawo ta daddage ta hada karfinta ta kifa masa mari mai kyau kamar yanda ya mata..
"tasssss! kake ji
Tunda aka uwarsa ta haifeshi yau ne rana ta farko da ya taba shan mari a rayuwarsa...
Ranshi yayi bala'in baci, idonshi ya koma jaa wur! Jijiyoyin kansa duk sun firfito...nuna kansa yake yana dad'a matsowa kusa da ita
"Ni?? "Mari?? Wow! Bravo alaikh! Ya fada yana tafa hannunsa
Tsoro ne ya kamata ganin in less than a minute gaba daya ya canza, itama duk tsiwarta bata taba zaton zata iya marin someone like him ba..
Rikota yayi da karfi ya matseta yana zare mata ido
"Ke wacece? Mai kike takama da shi? Waye ubanki a kasannan da har zaki daga hannu ki mareni..
Gaaba daya ta gama tsorata..jikinta sai rawa yake amma sai faman dakewa takeyi ita ala dole she's strong....sai kokarin kwace kanta take daga rikon da ya mata dan ji take wajen har ya fara tsami
"Ka sakeni, you are hurting me...ta fada tare da tufar da yawo a gefenshi
Ya ilahi! Abunda ya tsana d most...yawu! Ma shi? Lalle yarinyarnan yau ta gama kai shi bango
"Ka sakeni nace ba! Ta sake fada da karfi
"So kike na barki? Zan barki but only on one condition shima dan na ganki mace kuma yarinya karama...i want you to kneel before me and prove that you are sorry!
Is he that serious..ta fada a ranta
Lalle ma wannan ya gama raina mata hankali...wa zaiyi kneeling a gabanshi, ba dai forhaana ba dai!
"Will you??
Har ta bude baki zata ce bazata yi ba kuma tayi wani tunani...
"Let go off my hands, i will...ta fada kamar fada kamar da gaske
Saketa yayi tare da fadin....
ohyaaaa!
Yana saketa kuwa ta yi cilli da takalmanta ta kwasa a darii Kamar wata sabon kare sai cikin gidansu zaituna....
Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, wannan aanya lafiyarta kuwa? Ji yanda take wani uban gudu kamar ba mace ba...Wato shi zatayi wa wayo koh!
Toh ta gudu kuma ta shiga gidansu idan yana da kokacinta binta zaiyi ya kakkarya mutumiyar banza....but his time are priceless and treasured, ba zai bata su akan yar yarinyar nan ba but duk randa ya hadu da ita She must say that 'sorry' she run because of.
Haka ya juya ya shiga motarsa yay mata key yayi tafiyarsa yana mai bakincikin wai yau shine har wata y'a mace ta mare sa. Shi da yake juyasu son ranshi yau mace har ta kwada masa marin da har yaji zafinsa...
•••••
*16*
•••••
"Haanar kice, amma ai kya bari na shigo ciki kamun ki cikan kunne ba" ta fada tana cire takalminta ta shigo..
"Yau kuma batar hanya kikayi ne ko mai
"Auu abunda ma zaki fada kenan ko..ni kinga tafiya ta ma, ta fada tana juyawa ta koma
"Mai yayi zafi daga tambayarki naga dai ba zuwar min kike ba, kodai daga gidansu mutumiyar taki kike ne?
"Ni kinga musamman na zo miki...idan kuma da surutu zaki tarbeni kinga sai in kama gaba kuma, inji forhaana
"Baza muyi haka ba...ki shigo tawan, ya gida?? Ya Amminki da Nana??
"Duk lafiyarsu kalau suna gaidaki na
"MashaAllah ina amsawa.
Suna zaune suna hiransu har wajen azahar ta tuna abunda Ammin ta fada mata akan kar ta jima..gashi ita ko gidansu Antyzainab din bata shiga ba tsohuwar nan rike ta da surutu, tsaki tayi tare da mikewa tayi sallah ta mata sallama akan idan ta tashi daga gidan bazata biyo ba wucewa zatayi dan ta jima...
"Toh ki gaishe min iyayen naki idan kin koma, ungo wannan ki kaiwa Naana ta mika mata wata keda kunshe kayan ciye ciye irin na y'an da....
"Wato ni banda ni ko??
"Ai na dau yau bakya bukata ne, gani nayi kina ta faman hada min rai ke gaki kinyi latti bansan ko tashi sama zakiyi ba...
"Hahahhh...mungode, wallahi banaso in naje can muna cikin hira da zaituna Ammi ta kira ni ne shiyasa nake sauri" forhaana ta fada
"Ni ai ba hiran nake miki ba..
"Hoooo tsohuwar nan rigima kike nema ni dai na tafi ta fada tana fita daga gidan da d'an gudunta.
•••••
Bayan ya fito daga bangaren Umminsa ne kawai ya yanke shawarar yau ya dan zaga _B Marwa motors_
Wajen kawunsa
Daman a shirye ya fito tsab yayi wankansa kawai wajen parking lots na gidan ya wuce..
Motoci ne atleast zasu kai 10 a wajen kala kala masu uban tsada ....na Amir daya, daya sienna ce Babba wadda ake yan makaranta, daya na Antyzainab, manya biyu na kawunsa sauran kuwa daman nashi ne shi ya kawosu suna nan duk wadd yayi niyar fita da shi ya dauka ya fita da shi.
Wajen wani BMW fari tas ya sha black tint naga ya nufa, remote ya danna ya bude ya shiga yay mata key...
•••••
Da d'an gudunta ta fito daga gidan ai sai ji kawai tayi "Pooooushhhhhh, ji tayi gaba daya jikinta an masa painti,mota ya tako ruwan ta'bo sai jikin bakar abayar da ke jikinta... Gaba daya jikinta ya koma ba kyan gani abunka da bakin abu....takaici, kuka, ihu ne ta rasa wanne zatayi
Shi kuwa daman ka'idarsa ce wannan, sam bai iya driving a hankali ba...yay wa motar key a guje ya fito kenan ya shige ciki tabon da ke kwance gefen kwalta...
Bai ma kula da aika aikar da yayi ba
"Shit! Kar dai dattin nan ya taba min jikin mota...ya fada yana wani yatsina fuska kamar wani kashi ne ya tabar masa mota
Ranshi bace ya fito zai duba jikin motar ya ga mutum tsaye gefensa duk ba kyan gani, tsorata yayi..kaiii kodai mahaukaciya ce ganin yanda duk fuskarta ya baci
"Hey! Mai ya sameki ke kuma? Ya fada yana dan d'aga murya
Ganin irin tambayan raini da yake mata ya sa ranta ya baci ta fara nufo inda yake kamar zata kife
Ai tuni cikinsa ya dau ruwa...kar dai mahaukaciya ce, amma mai zai kawo mahaukata layin nan kuma, yake tambayar kansa dan shi sam baya son ko ganin mahaukata dan yana shakkarsu
"How dare you? Kai makahon inane?? Eyyeeee? Ta fada da karfi yayinda ta iso daf da shi kamar mai shiga cikinshi babu ko shakka a idonta..."
Shi abun mamaki ma ya basa, kuji yar yarinyarnan dan karfin hali ta zo tana rafka masa uban ihu kamar tsaranta..toh in laifin ya mata sai me! Har ta isa ta daka masa uban tsawa haka..anya kuwa ba mahaukaciyar bace? A'a ai da mahaukaciyace bata da hankalin kwata wa kanta hakkinta...shi kadai yake tunanin nan a ransa
"Wait, malam magana nake maka ka kafe ni da ido kana kallona, baka ga aika aikar da kamin bane ko kuwa?? Idan baka iya tukin bane dole sai kayi ne, kaje kana son illata mutane..ni Allah ne ma ya cecen da ba ka taka ni ba. Anya kuwa ma ba wani abun ka sha kamun ka fito ba"...cikin isa da rashin kunya duk take maganan....
*18*
Tsakaninta da Allah ta kwasa a guje tayi cikin gidan, mai gadi na mata ihun ta tsaya amma ko ta kanshi ba ta bi ba...a guje tayi bangarensu zaituna ta banko musu kofa ta shiga a dari...Allah ya taimaketa Antyzainab bata nan tana can bangaren ummin behzad balle ta sha tambaya
Zaituna na kallo a falo sai ji tayi an banko musu kofa an shigo...juyowarta ta yi ido hudu da forhaana caba caba ba kyaun gani, da sauri ta iso wajenta tana tambayarta mai ya faru haka
"Madam matsa min naje na watsa ruwa a jikina na canza kayannan tukun wlhi duk jikina kaikayi yake....ta fada tana nufar dakin zaitunan
"Muje toh..inji zaituna dan tasan halin kawar tata sarai yanzu sai tayi zuciya
Ta shiga tayi sabon wanka zaituna ta bata daya daga cikin Abayanta ta saka tsab ya zauna mata dan girman jikinsu kusan daya ne..
"Wai ni baki fada mini mai ya koro ki har kika fada a kasa haka ba...zaituna ta tambaya dan ita duk a zatonta faduwa foorhaanan tayi
"Ke kuma sai ce miki faduwa nayi,
Nan ta kwashe abunda ya faru da ita gab ma daya ta fada mata har da kwatan ta mata yanayin saurayin da sukayi fada
Baki zaituna ta sake galala tana binta da kallo
"Aaah kin cece kanki wollah da kika gudu..waiii! Kinma san wa kika mara kuwa?
"Waye? ta tambaya
"Yayanmu Babba dai da kike jin labarinsa wajena, _behzad_
Hannunta ta daura kanta tare da zaro ido....sai kuma tayi wani tunani ta yatsina fuska ta ce "koma dai wanene ni dai nasan na rama kuma dole yaji yanda naji nima.
"Amma dai kinsan baki kyauta ba ai
"Koma mai ai shi ya mun laifi..ta fada tare da mikewa tana shirin fita
Bangaren ummi sukaje inda Antyzainab taje, sun samesu su uku har da mahaifiyarsu Amira (antyfatima) suna hira gameda bikinsu Amira da za'ayi dan duk a rana daya za'ayi da na NanaAisha yar forhaana
Sa'konda Amminta ta taba ta mika wa Antyzainab cikin girmamawa
"Kai Amminku da son bidi'a take! Ni da mukayi walima da wushe wushe kadai zamuyi shine ta je tayi organising su Dinner da mother's night....ungo duba kuga ga abunda Bilki ta hada' ta fada tana mika musu wani rolled golden colored kwali da aka saka su invitation cards din a ciki
Karba sukayi suna gani, ikon Allah!
"to ai bai baci ba, kinga duk sai a hada a yi tunda wannan shine farkon aurar da y'ay'anmu.....inji mahaifiyar behzad
Zaituna da forhaana na gefe dadi kawai ke cinsu ta kasa ba damar nunawa fili...sun bala'in cin burin auren nan daman, abunda ya sa su yin sanyi daman jin baza'ayi wani shagali sosai ba...haba yanzu sukaji sa'ida
Mikewa sukayi suka yi musu sallama akan zata tafi..kudin mota ummin behzad ta miko mata amma kememe taki karba, da ta ga da gaske dai bazata karba ba ne ta bawa zaituna idan sun fita ta bata
"Yarinya mai hankali da nutsuwa...ta fada bayana sun bar falon
"Ai yaran bilki ba dai tarbiya ba kuwa..inji Antyzainab
"Ai kuwa! Allah ya raya ya basu mazaje na gari
"Amin" suka fada a tare.
•••••
Suna fita suka wani sake uban ihu...wai! Ai kuwa za'ayi casu
"Addu'anmu ya kamasu..kinsan ni Ammi bata fada mana cewa za'ayi events haka ba, yanzun tukun nake ji ai da na jima da fetsa miki
"Hahahhh...ki bari kawai, kinga ba bata lokaci yanzu mu fara shirye shiryenmu kawai tunda saura kwana hudu already kayanmu daman yana nan...
"Ba sai kin fada ba, ni yanzu bari na je na canza kayana kasancewar sai da suka bayar a wanke kamun suka fito wajesu AntyZee.... na wuce kar Ammi ta ce na jima kuma wataran a hana ni fita...inji forhaana
"Tohm, muje in raka ki
Haka suka jera sukaje ta raka ta ta hau adaidaita sahu ta wuce gida ta ma manta da batun wani fadan da tayi dazu....
.
*deejatou*
Comments
Post a Comment