Kauna ce sila

*KAUNA CE SILA💝*

*written* *by* *:* *khadijah* *Tijjani*

            *11*

     

      Bayan sun gama gaisawa ne ya gabatar musu da batun da ya kawo shi....khadija ba kamarin kaduwa tayi ba, tana mutuwan son d'an nata.....rokonshi ta shiga yi tana kuka.
    "Ku taimaka ku bar min behzad, wallahi shi kadai nake gani in samu sa'ida...Allah yayi bazai rayu da mahaifinsa ba, bai san dadin uba ba, yanzu kuma ku zo ku rabashi da mahaifiyarshi...wani irin rayuwa kuke so d'an nan ya tashi a ciki.
   
      Ganin yanda ta kidime take magana ya sa ya katseta..yasan duk cikin soyayyar uwa ce, yasan yanda uwa ke son yayanta..shima gaskiya ba dan an fi karfinsa ba bai goyi bayan a raba ta da d'anta ba..
     "Kwantar da hankalinki khadija, ba wani za'a bawa rainon yaron nan ba...MamaBabba da kanta zata rike shi, kuma kinsan yanda take sonshi bazata bari wani abun ya sameshi ba....tarbiya kuwa kema mai iya shaida ce akanta, inshaAllah danki bazaiyi irin rayuwar da kike tunani ba....
     "Kuyi hakuri, ba wai na raina ta bane, ko kuma ina nufin bazaku bashi kulawa mai kyau ba ne....shuru tayi kuma kamar mai tunani,
    Can ta kuma cewa" ni dai ku taimaka kar ku raba ni da d'ana
    
    Bayani ya kuma yi mata..ba yanda za'ayi ne behzad ya zauna wajenta, ko ya koma Mamababba zata zo da kanta, gwara kawai ayi zuwa daya..
   
   Khadija kiyi hakuri ki basu d'annan, na fahimci damuwanki...na san kina son d'anki, amma dole daman wataran zaki rabu da shi..dole yan'uwan ubanshi su amshi dansu...mahaifiyar ta fada cikin tausaya wa y'arta.
  
    "Bazan iya rabuwa da d'ana ba....zan bi shi mu tafi tare, zan zauna in kula da d'ana a can wajensu...d'ana bazaiyi maraicin uwa ba...
   Katseta mahaifiyarta tayi  "kinsan mai kike fada kuwa, zaki bishi kamar ya? Ke kenan haka zaki zauna? Ko bazakiyi aure bane? Kinsan ko kin bi su in dai kika tashi yin aure toh dole ne su karbi d'ansu dai ko...??

    "Na sani! Zan zauna da d'ana, na hakura da yin auren....zan sadaukar da komai in dai akan behzad ne...ta fada ba tare da tunanin komai ba
      Aboubakar kallon ta kawai yake yana mamakin irin karfin hali nata, mamakin yawan son da takewa behzad yake...kodayake ba abun mamaki bane! Kadan kenan daga cikin son da uwa ke wa d'anta

    "Kin yadda zamu tafi tare da ke? Kuma kina ganin ba wata matsala?
   Juyowa tayi tana kallon mahaifiyar ta alamun tana neman amincewarta.....kai mahaifiyar tata ta daga mata cikin tausayawa' alaman tayi supporting na batun na yar ta ta.
   
    "In dai tafiyar taki shine zai zama kwanciyar hankalinki  kije...kije ki kula da danki, kar ki bari yayi rashin iyaye..Allah ya miki albarka, ya sa d"anki mai biyaye ne. Abunda mahaifiyarta ta iya cewa kenan

      Kallonsu kawai yakeyi yana mamakin mutane masu tausayi da son y'ay'a irinsu...irin wannan al'amarin ya sha faruwa a wajejenmu, amma wasu matan su da kansu suke kai y'ay'ansu su dungurar wajen yan uwan uba, kaga yaro ya tashi ba tarbiya ba ilimi...amma ita wannan har za ta baro kasanta ta zo inda ba ko dan'uwa daya musamman ta zauna dan ta kula da d'anta kwaya daya, lalle ta cancancu yabo! Abunda tayi ba karamin burge shi yayi ba..

    "Yaushe ne tafiyan?? Ta tambaya cikin sanyin murya...
"Nan da kwana uku inshaAllah.
    Toh Allah ya kaimu"
"Amin" ya fada shima

    Behzad ne ya shigo a guje sanye da uniform na makaranta, yaro fari tass kwakkyawa da shi, yayi girmanshi yayi wayo abunshi kamar ba dan jaririn da ya sani ba...gudu yake yana dariya baya ko kallon gabansa....a take Aboubakar yaji yana jin son d'an dan'uwan nashi...kuma ya samu kwarin gwiwan tafiya da shi dan yaron akwai shiga rai.

     "Behzad! Ya kirashi
  Na'am ya amsa cikin harshen larabci ba tare da kwiya ba yaje wajenshi ya zauna na gefen kujeran da yake kai.

   Toh fa..ya fada a raina! Inaji yaron nan banda larabci ko turancin ma ba ji yakeyi ba, lalle zasu sha fama da MamaBabba...ya fada a ranshi yana murmushi

      
       Bayan sun sha hira ne yayi musu sallan akan su shirya nan da kwana uku zai zo su wuce.........

•••••

   Love you all❣

   XOXO💋

*deejatou*

Comments

Popular posts from this blog

Kauna ce sila 31

Kauna ce sila 33.34.35

Kauna ce sila