Kauna ce sila

*KAUNA CE SILA💝*

*written* *by* *:* *khadijah* *Tijjani*

            *09*

  

      Ganin bashi da wata mafita ya sa ya fara magana kamar shima zai fashe da kuka  "ku kwantar da hankalinku...komai ya faru da mutum toh Allah ne ya kaddara masa, kuma yadda da kaddara mai kyau da mara kyau yana daya daga cikin cika cikan muslunci..
  "Kai d'an nan, kana tsinkar mini zuciya fah..wani abun ne ya samu Aboubakar din? Ta tamabaya...
"A'aa! Su Alhaji ne dai...ya kasa karasar wa yana zubda hawaye
   "Mai ya faru da su? Duk suka hada baki suna tambaya
   
    "Plain crash, hatsari sukayi...they had an accide....bai iya karasar wa saboda ganin yanda MamaBabba ta wani yi zaman bori a kasa..
  
  "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Abunda khadija ta iya fada kenan kawai ta tsuguna a wajen jin yanda cikinta ya wani murde ta
Zainab ma sulalewa tayi a wajen ta saki kuka...fatima kadai ta iya karfin halin tambayan halin da suke ciki
   "Ina suke yanzu??
"Wani hali suke ciki??  Abun da ta iya tambaya kenan

    "Allah ya musu cikawa...Allah ya karbi abunsa...ya fada yana zubda kwalla
   Dukkansu ba mai iya taimakan juna, kowa yana durkushe daga mai kuka sai wanda kukan ya gagareshi
  Nishi nishi suka ji, ganin ya fara yawa ya sa suka juya....khadija suka gani durkushe a jikin hannun kujera, ta kasa tsayuwa ta kasa zama....MamaBabba na ganin halin da take ciki ta gane nakud'a take
   Tashi tayi ta je wajenta cikin sauri
   "Fatima rike mini ita"
Haka suka rirriketa suka kaita dakin ganin yanda nakudar ya zo mata gadan gadan
    Ba'a dau minti goma ba ta santalo y'ay'anta guda biyo mace da namiji inda macen ta fito ba rai....yaron kadai ke da rai
    Kana ganinshi sak mahaifinsa kawai hasken mahaifiyarsa ya dauko da yanayin gashin sa, kowa tausayin d'an da mahaifiyarsa yake...a ranar da ya zo duniya a ranar mahaifinsa ya rasu...

  
     Suna gamawa kimtsa mai jego da d'anta aka shigo da gawan Alhj Marwa da Abduljalal..
Allahu akbar, masoyan wannan bayin Allahn ba wanda bai jijjigu da jin rasuwarsu ba.
    Iyalansu kuwa har yanzu banda MamaBabba ba wanda yake iya ko da karban gaisuwa, itama karfin hali takeyi Allah kadai yasan yanda take ji a ranta
  
   Khadija na gefe rike da d'anta, tausayinshi da ita kanta take....a lokaci daya labarin mutuwan mijinta da mahaifinta ya riske ta ga sirikinta.

_bayan sati daya_  yaro ya ci suna *Behzad*....sunan da mahaifinsa tun yana raye yayi niyyan saka masa kamar yanda khadija ta fada.
     Yaro shuru kullum kamar ya san  abunda yake faruwa cikin gidan nasu...baya yadda da kowa, daga mahaifiyarsa sai MamaBabba..hatta zainaba duk nacinta na son daukan shi haka take hakura ta barshi.

•••••
    _Bayan kwana arba'in_

  Rayuwa ta ci gaba da tafiya wa wad'annan bayin Allah cikin hakuri da juriyar rashin da sukayi.
     An raba gado kamar yanda addinin muslunci ya tsara....An ba wa Aboubakar kason sa, na Abduljalal kuwa MamaBabba ta damkawa Aboubakar amanar dukiyar *behzad* da zainab ya rika juya musu har zuwa lokacin da zai mallaki hankalinsu.
   
   Bayan khadija tayi Arba'in ne ta tafi Madina zuwa duba mahaifiyarta....MamaBabba ba dan ta so ba ta yarda ta tafi kasancewa sun sha'ku sosai da behzad, kusan kullum yana bangarenta..shan nono kadai ke kai shi wajen mahaifiyarshi.

     Shuru shuru bayan ta tafi ba ta komo ba, gashi yanzu ana neman kusan shekara...hankalin MamaBabba ya tashi
"Ba dai Khadijah tafiya tayi da yaronnan ba?
Ita dai ba za ta iya rabuwa da behzad ba gaskiya, ta rasa mahaifinshi ga shi shima ana so a raba tada shi.....A'aa gaskiya da sake!

*deejatou*

Comments

Popular posts from this blog

Kauna ce sila 31

Kauna ce sila 33.34.35

Kauna ce sila