Kauna ce sila

*KAUNA CE SILA💝*

*written* *by* *:* *khadijah* *Tijjani*

            *10*

  
         _"In their hearts there is a disease and Allah (SWT) has increased their disease. There is a painful punishment for them because they lie"_   Al-bakarah #10
   

_bayan sati biyu_

          Mamababba zaune ita kadai a bangarenta...zaman kadaicin nan ya fara isanta, ga zainab ma ta samu admission a skul of nursing ita da Bilkisu...sun tattara sun je hostel a cewarsu zasu fi karatu sosai..               Haka ba dan ta so ba ta barta ta tafi....kullum ita kadai a bangaren nasu kamar wata aljana....gaskiya ita hakurinta ya fara karewa.

     Fatima ma ba ko da yaushe take zuwa ba yanzu...da khadija na nan ne ma da sun debewa juna kewa. Abunda take ta sa'kawa a zuciyarta kenan

     Sallama yayi ya shigo, sun gaisa ke tambayarsa ya aiki da kuma fama da jama'a kasancewar tun da abduljalal da mahaifinsa suka rasu komai na gidan da dukiyarsu ya koma hannun Aboubakar din

      "Alhamdulillah, gashi muna fama "
 
   Allah ya taimaka ya kuma shige gaba"
           "Amin"

    Sun dan taba hira,  haka yake...kullum da safe sai ya shigo mata yaji ko tana da bukatar wani abun haka da dare zai zo ya mata sallama....ita dai tana jin dadin yanda yake kula da ita gaskiya
        "Mama bari in wuce" ya fada yake tare da mikewa

        "Zauna Aboubakar, so nake muyi magana ita ma ta fada in a serious tune....
    Komawa yayi ya zauna tare da mayar da hankalinsa kanta
      
        "So nake kaje ka dauko mun jikana...
     Cikin rashin fahimta yace "jikanki kuma Mama, wanne??
     "Ina da wani jika ne da ya wuce dan gidan marigayi, ta fada tana watsa masa kallo

       Ya ilahi! Wani rigima kuma mama take son tadawa..
      "A'a...mama da dai kin bar batun nan, yaron da koh shekara biyar baiyi ba, idan aka kawo miki shi ya zakiyi yanzu?? Ke da girma ya fara zuwar miki...

   "Ku da na haife ku ai wani ne ya rainar mini da ku" ta yi saurin katseshi tun kamun ya rinjaye ta

  Ganin yanda ta fara daukan batun da zafi ya sa ya sassauta murya "mama yanzu dai kiyi hakuri, idan ya cika shekara biyar da kaina zanje in dauko miki shu nayi miki alkawari..
     "Za ka je ne, ko kuma ba za ka je ba in tafi da kaina....ai ba sabon waje bane a wajena, kawai dai na ga ina da wanda na isa da shi shiyasa nayi maka magana, ko so kake taje tayi aure jinina yayi rayuwa a gidan wani bayan yana da gata da yan'uwa....amma idan ba za ka je ba ba sai ka tsaya bani shawara ba...ta fada a dan harzu'ke

     "Kwantar da hankalinki, a gobe zan fara shirye shiryen tafiya inshaAllah...ya fada ba dan ya so ba
  
      Fad'ad'a fara'arta tayi..hakorin nan kamar zasu zube k'asa
   "Yauwaa d'an nan...Allah maka albarka, na gode!
   "Amin" ya fada tare da mikewa ya mata sallama ya tafi yana mai mamakin irin son yara da mahaifiyar nasu takeyi da har ya mantar da ita da idan ita ne a halin khadija ya za ta ji idan aka raba ta da dan d'anta mai shekara hudu..
     
  
•••••

     Jikanta kawai take jira, ta gama kimtsa komai...musamman daki daya ta cika masa da kayan yara na wasa da na karatu.
     Zainab ta zo gida hutu, itama tayi murnar dawo da behzad da za'ayi
   "Mama ba ko nima sai in kula da shi ba, ta fada cikin jin dadi

    "Eh! Da ya ke a gidan zaki dawwama ba...ni fa yanzu ma ji nake kamar a kaina kuke wlhi, kuyi ku gama daga ke har bilkisun mu aurar da Ku, kamun ku zo ku zama mana jidali
   "Mama mune zamu zamar muku jidali, ta fada kamar zatayi kuka
    "Eh! Ta mayar mata da amsa tana ci gaba da aikin da take
     Ita kuwa tashi tayi fuuuu ta bar side din taje gaida Auntyfatima kamar yanda take kiranta

•••••
     Kwanansa hudu a Madina amma ya rasa ta yanda zai tunkari khadija da mahaifiyarta  da maganan tafiya da behzad da yayi....shikam gaskiya Mama ta sa shi abun kunya yake gani
   Da wani ido ma zai kallesu yace ya zo tafiya da d'an  nasu duk irin zaman dad'i da mutunci da akayi...
   
    Haka ya daure washegari ya je gidan nasu...sun mishi tarba na girma da arziki
Khadija bata kawo komai a ranta ba, ita duk a tunaninta ya zo umrah ne ya wuce ya kawo musu ziyara....

•••••

     Love you all❣


*deejatou*

Comments

Popular posts from this blog

Kauna ce sila 31

Kauna ce sila 33.34.35

Kauna ce sila