Kauna ce sila 33.34.35
[9/27, 9:17 PM] Sis Salmat: *KAUNA CE SILA💝* *written* *by* *:* *khadijah* *Tijjani* *34* ••••• Can gidan su forhaana kuwa anyi cigiyar anyi har sun gaji ba labari sai kawai suka dukufa wajen Malamai akan a taya su da addu'a Allah ya bayyanar da ita kuma duk an basu tabbacin nan ba da jimawa ba zata bayyana.. Zaitunah da Ummin behzad kuwa tun da abun ya faru ba Kansu suna can gidansu forhaana ana ta cigiyar da su haka zasu wuni zagaya gidan abokan arziki da yan'uwa ko za'a sameta da daddare kuwa su kwana addu'a da nafilfila Amarai kuwa suna can gidajensu ba wanda ya fad'a musu ko ya basu lbrin abunda ya faru dan gudun tashin hankalinsu.. •••• Zaune suke a parlor'n gidan, Ammin, Ummin behzad, Zaitunah, AuntyFatii(matar kawunsu Z...